Asalin hoton, Youtube
Har yanzu akwai jaruman Kannywood aka daina jin ɗuriyarsu tun bayan da masana'antar ta fara rarrafe saboda taɓarɓarewar tattalin arzikinta, wanda ya sa aka rage shirya finafinai.
Rashin kasuwancin finafinan ya sa masu shirya fina-finai da dama suka koma wata harkar.
Ana tsaka da haka ne aka buɗe sinima a Ado Bayero Mall, inda furodusoshi suka fara gwaji ko zai haɓaka masana'antar, amma hakan bai ciyar da masana'antar ba.
Hakan ya sa aka koma ɗora finafinai a YouTube, wanda hakan ya sa masana'antar ta fara farfaɗowa, har ake ganin masana'antar ta fara komawa da ƙarfinta.
Wannan ya sa BBC ta zaƙulo wasu jarumai, waɗanda a sanadiyar finafinai masu dogon zango, suka farfaɗo:
Hadiza Kabara
Asalin hoton, Youtube/Arewa24
Hadiza Kabara ta kasance ɗaya daga cikin jarumai mata sahun farko a masana'antar Kannywood.
A farkon fara fitowarta, ta riƙa fitowa ne a matsayin budurwa, inda taka rawa da tsoffin jaruman masana'antar irinsu Musbahu Ahmad da Saima Muhammad da Fati Muhammad.
Daga baya jarumar ta yi ɓatan-dabo a masana'antar, inda aka ɗauka ta janye jiki daga harkar fina-finan.
To sai dai bayan bayyanar fina-finai masu dogon zango jarumar ta yi fitowar murucin kan dutse - da Hausawa ke yi wa laƙabi da ''bai fito ba sai da ya shirya'' - domin kuwa ta kasance cikin manyan jaruman da suka fi taka rawar gani fina-finai masu cin dago zango.
Ta fito a fim ɗin Daɗin Kowa da tashar Arewa24 ke shiryawa a matsayin ''Lantana mai adashe'', sannan tana cikin jaruman shirin Gidan Badamasi, inda ta fito a matsayin ''Hauwa Alhaji Badamasi''.
Kuma jarumar ta taka rawa gani a duka waɗannan fina-finai, kuma watakila hakan ba ya rasa nasaba da kasancewarta tsohuwar jaruma da ke da ƙwarewa.
Bashir Bala Chiroki
Tsohon jarumi ne da ya kware a fannin kitsa tuggu amma a cikin fim.
Ya fito a tsoffin fina-finai da suka yi farin jini a baya wajen masu kallo, irin Sangaya da sauransu.
Bashir Bala Chiroki fitaccen jarumin barkwanci ne da ya shahara a shekarun baya.
Sai dai bayan wasu lokuta jarumin, ya ɓata a masana'antar, inda har masu kallo suka riƙa cigiyarsa.
Jarumin ya taɓa fitowa a kafofin yaɗa labarai ya ce ya koma tallan kunun aya bayan da furodusoshi suka daina sanya shi cikin fina-finansu.
To amma shirin 'Gidan Sarauta' na Abubakar Bashir Maishadda ya maido da jarumin cikin sana'ar, inda ya fito a matsayin wani bafade mai ban dariya a cikin cikin.
Mustapha Musty
Asalin hoton, Social Media
Mustapha Musty na daga cikin jaruman da suka ja zare a masana'antar Kannywood, musamman tsakanin shekarun 2000.
A lokuta da dama yakan fito a matsayin jarumin da ke taimaka wa babban jarumi, kodayake a wasu fina-finan yakan fito a matsayin babban jarumi.
Bayan wani lokaci jarumin ya yi kusufi a masana'antar, inda aka nemi shi aka rasa.
To amma bayyana fina-finai masu dogon zango sun farfaɗo da shi, inda aka ganshi a fim ɗin Kwana Casa'in na Arewa24 da kuma fim ɗin Garwashi na kamfanin UK Entertainment.
Magaji Mijinyawa
Asalin hoton, Youtube/Dorayi Films TV
Magaji Mijinyawa ya kasance cikin jaruman da ke fitowa a matsayin iyaye.
Jarumin ya kasance ɗaya daga cikin tsofaffin taurari masu ƙwarewa a masana'antar, inda yake taka rawa daban-daban da aka buƙace shi ya fito.
Kamar sauran takwarorinsa da suka koma gefe a masana'antar, an ɗauki dogon lokaci ba a ga jarumin ba, kafin ya bayyana shirin Gidan Badamasi mai farin jini.
Magaji Mijinyawa ya fito a matsayin Alhaji Badamasi a shirin, wani hamshaƙin attajiri, kuma matsolo da ba ya son ganin kwabonsa ya kuɓuce masa.
Nura Dandolo
Asalin hoton, Dorayi Films/Youtube
Nura Dandolo, kamar yadda aka san shi a baya, lokacin da yake fitowa a fina-finai kafin ya ɓuya.
A farko yakan fito ne a matsayin mai barkwanci a fina-finan Ibro, inda ya yi fice wajen kaɗa kacakaura tare da yi wa mutane ba'a.
Sai dai bayan wani lokaci a daina ganin jarumin, inda har wasu ke tunanin ya daina fitowa a fina-finai.
A amma jarumin ya waiwayo masana'antar, a cikin shirin Gidan Badamasi mai dogon zango, inda ya fito a matsayin Yaya Ɗankwambo, wato babban ɗan gidan Alhaji Badamasi.
Yaya Ɗankwambo, kamar yadda ake kiransa a cikin fim ɗin na daga cikin taurarin da suka fi farin jini a fim ɗin.
Lawan Ahmad
Asalin hoton, Lawan Ahmad/Facebook
Lawan Ahmad jarumi ne da ya daɗe a masana'antar Kannywood yana finafinai, amma fitowar wasu matasan jarumai ta sa ya ɗan koma gefe, har ya koma siyasa gadan-gadan.
Amma daga bisa fim ɗinsa na Izzar so ya dawo da shi ƙadami. Fim ɗin na cikin finafinai masu dogon zango da aka fi kallo a YouTube.
Tijjani Asase
Asalin hoton, Tijjani Asase/Facebook
Tijjani Asase shi ma jarumi ne da ya daɗe a masana'antar, amma dawowarsa a fim ɗin A Duniya ya dawo da shi harkar sosai, inda fim ɗin ya canja harkar dabanci a finafinai.
Bayan wannan Tijjani Asase ya fito wasu finafinan masu dogon zango, irin su Ɗan jarida da sauransu.
Tijjani Faraga
Asalin hoton, Abubakar Bashir Maishadda/Facebook
Tijjani Faraga shi ma jarumi ne da ya fara fim tun ana harkar a daɓe a Jos, amma daga baya tun daga fim ɗin Labarina da Manyan Mata, sai ya ƙara haskawa a masana'antar.
Isah Ferozhkan
Asalin hoton, Isah Ferozkhan/Facebook
Isah Ferozkhan, wanda aka fi sani da presido, shi ma ya daɗe a masana'antar. Amma fitowarsa a shirin Labarina mai dogon zango ya taimaka wajen dawo da shi.
Bayan Labarina ya fito a finafinai irin su Manyan Mata da Garwashi da sauransu.
Shuaibu Lawal
Asalin hoton, Abubakar Bashir Maishadda
Shuaibu Lawal shi ma jarumi da ya daɗe yana fitowa a finafinai musamman na dabanci, amma finafinai irin su A duniya da Ɗanjarida da Manyan Mata sun ƙara farfaɗo da jarumin.
Akwai sauran jarumai irin su Zahradden da ya ɗan koma gefe a masana'antar, amma yanzu ya dawo a fim ɗin Labarina, da Zama da zargi da ke cikin Taskar Kannywood na Abdul Amart, wanda za a fara haskawa nan gaba da Rahama MK ta Kwana 90 da wasu jarumai da Auwal Isa West da Ramadan Booth da Teema Makamashi da wasu da dama da suka fara fitowa a finafinai, kuma ake tunanin za a cigaba da ganinsu.